Responsive Ads Here

Tuesday, 12 November 2019

TALAKKA BAWAN ALLAH


LAGOS/KADUNA ROAD

Bismillahirrahmanirrahim
Ina mai farawa da Godema Allah da yabamu Aron Rayuwa Muka ga wanna Rana mai Albarka inason inyi Dan takaitaccen Rubutu game da Hanyar Legos Zuwa Kaduna
Wannan Hanyan Babban Hanyace Wadda Take Hada Arewacin Najeriya Da Kudancin Najeriya,Amman Wallahi akullum Sai Ansamu Hasarar Dukiya Mai Yawa awannan Hanyan
  {1} TEGINA ZUWA MAKERA
 Tafiyace Wanda idan Hanya Nada kyau Baiwuce 45mints ko ince kilomita 100 Amman Ayanzun Ko Direba Naso Ko Baiso Karamar Mota sai Yashafe Awa Biyu koma fiye da haka Shikuma mai babban mota sai ya shafe kwana biyu koma sama da haka kuma hannusa a gaba domin yana tsoron ya lake ko ya fadi wa yennan wajajen sun hada da:
1.Gadar Gulangi (Bakar Gada) Iyakar Mashegu da Rafi LGA
2.Unguwar Gwari,tsakanin Gidan-kwano da Gobirawa a Mashegu LGA
3. Gab da Shiga Gadar Kasanga akwai Wani Wuri Ana kiranshi Bus-stop Mashegu LGA
4.Kanafito wa Gadar Kasanga Dai dai kwanar Kasanga Ahalin yanzu yafi ko'ina muni  Duk a Mashegu  LGA
5.Akwai Wani wuri inda Akecema Marwa,inkafito Kasanga Kafin kashiga Rafin-gora
6.Akwai Wani Wuri Mara kyau tsakanin Tsakanin Rafin-gora da Tanangi shima Akwai Wani Wuri Mara Kyau
7.Sannan Akwai Wata Gada Gab dashiga Tanangi Gaskiya wannan Gadar takusa Karyewa kuma idan har wannan Gadar takarye tabbas wanna Hanyar  Tamutu Gabadaya domin Babu wurin Rabawa.
{2} MAKERA ZUWA MOKWA
1.Sabowar Makera shima wanna wajen yazama Wurin Cin Abincin Matasa majiya Karfi Kutigi LGA
2. Akwai wani waje cen gab da shiga Bokani Ana kiran shi Unguwar Dukkawa Mokwa LGA
3.Akwai wani waje idan kawuce Bokani yau sama da shekara Biyu ke nan Ana gyara Amma haryanzu Ba'a gama ba Allah ya sawaka.
 Talakawa da yawa suka dogara da kansu tahanyar kasuwanci akan wanna hanya Amma Abun Bakin ciki dayawa wasu sun karye sakamakon lalacewar wanna hanya wasu kuma sun canza Gari. Mafi yawan mutanen da ke zaune akan hanyar ba ma'aikatan gwabnati bane yen kasuwane da Manoma,  Sun taka rawar Ganin su kwarai da gaske waje gani sunyi Zabe alokacin Zabe musamman Wajen Kafa Jam'iyya mai mulki a yanzu wato APC sai dai kash...  basu morema zaben nasuba.
 TAMBAYA ANAN
1. Shin Gwabnatin Jahar Niger da Ta Nigeria Tana da anfani ga mutanen wanna yaki?
2.Koko Mutanen wanna yanki sunada anfani ga gwabnati?
Allah yasa wanna korafin namu ya kai ga kunnuwan wayenda yakamata kuma Allah ya basu ikon gyarawa Ameen summa Ameen.

No comments:

Post a Comment