LAFIYA UWAR JIKI
Yau xamuyi magana akan cututtukan da suke takuramana a wannan lokaci
BISMILLAHIR RAHMANIRAHIM
Cututtukan da ke addabar al'umma da ake
kamuwa dashi ta hanyar jima'i sune:
1.Syphilis
2.Gonorrhea
3.chlamydia
4.Genital herpes
5.Candidiasis
6.Trichomoniasis
7.Hepatities B&C (HBV&HCV)
Dss
Ayau zan dauki daya daga ciki nayi bayani
akansa.
"SYPHILIS"
1.SYPHILIS:cuta ce daya daga cikin cutuka
masu yaduwa ta hanyar ajima'i,veginal
sex,anal sex,oral sex.wannan cuta takan
kawo illoli ga jikin d'an adam,takan kama
wurare da dama kamar cikin farji,tsakiyarsa da
kuma wajen sa,mahad'ar mahaifa,cikin
baki,kan harshe da kuma al'aurar maza.ita
wannan cuta bata tsaya anan ba idan ta
kama mace mai ciki takan kashe yaro
acikin Mahaifa,ko asamu miscarriege.
Syphilis wata kwayar cuta ta bacteria ke
haddasa ta mai suna; "Spirochete Bacteria
Treponema Pallidum".ita wannan kwayar
cuta tana da matukar illa ga dan adam.
Musamman ga mace mai juna biyu idan tana
dauke da wannan cuta bataje dakin gwaje-
gwaje angano da wuri an magance balallai
wajen haihuwa takan iya gogawa jaririnyta
cutar ya zamto "Congenital Syphilis".
**ALAMOMIN TA:
1.Fitar kananan kuraje a gaban mace ko kan
al'aurar maza ko dubura.nawasu lokuta
sannan yabace ba tare da ko ansha wani
magani ba,amma fa tana nan cikin jini
2.fitan kuraje a tafin kafa da hannu ko fuska
ko ma wasu sassan daban marasa zafi ko
kai-kai shima nawani lokaci yabace batare
da ansha wani magani ba
3.zubar gashi,zazzabi,kasala,murar makoshi
**ILLOLIN TA:
Takan kawo matsalar kwakwalwa,kunnu
wa,gabobi,zuciya,hanyoyin jini da
ruwa,kasusuwa da sauran su,idan har ba'a
magance ta ba takai wasu shekaru ajikin
dan adam.
**HANYOYIN KARIYA:
1.Zuwa asibiti don gwaji musamman ga
mata masu ciki
2.Barin neman matan banza ko namiji ya
nemi namiji dan uwansa (zina ko luwadi)
Allah yakare mu.
3.Ga ma'aurata amfani da condom yayin
saduwa idan ta zama dole kenan
Allah ya kiyayemu ya bamu lafiya.

No comments:
Post a Comment